Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 40:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.”Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”

9. Saboda haka, shugaban masu shayarwa ya faɗa wa Yusufu mafarkinsa, ya ce masa, “A mafarkina ga kurangar inabi a gabana.

10. A kurangar akwai rassa uku. Sai ta yi toho, ta huda nan da nan, ta kuma yi nonna, har suka nuna suka zama inabi.

11. Finjalin Fir'auna na hannuna, sai na ɗauki 'ya'yan inabi na matse su cikin finjalin Fir'auna, na sa finjalin a hannun Fir'auna.”

12. Yusufu ya ce masa, “Wannan ita ce fassararsa, rassan nan uku, kwana uku ne,

13. bayan kwana uku Fir'auna zai ɗaukaka ka, ya komar da kai matsayinka, za ka kuma sa finjalin Fir'auna a hannunsa kamar dā lokacin da kake mai hidimar shayarwarsa.

14. Amma ka tuna da ni sa'ad da abin ya tabbata gare ka, sai ka yi mini alheri, ka ambace ni a wurin Fir'auna, har da za a fisshe ni daga wannan gida.

15. Gama ni, hakika sato ni aka yi daga ƙasar Ibraniyawa. A nan kuma ban yi wani abin da zai isa a sa ni a kurkuku ba.”

16. Sa'ad da shugaban masu tuya ya ga fassarar tana da kyau, sai ya ce wa Yusufu, “Ni ma cikin nawa mafarki, na ga kwanduna uku na waina a bisa kaina.

Karanta cikakken babi Far 40