Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 4:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.”

2. Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.

3. Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona.

4. Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa,

5. amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.

6. Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi?

7. In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”

8. Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi.

9. Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?”Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”

10. Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.

11. Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka.

12. In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”

Karanta cikakken babi Far 4