Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 35:25-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. 'Ya'yan Bilha, kuyangar Rahila, su ne Dan da Naftali.

26. 'Ya'yan Zilfa, kuyangar Lai'atu, su ne Gad da Ashiru. Waɗannan su ne 'ya'yan Yakubu da aka haifa masa a Fadan-aram.

27. Yakubu kuma ya zo wurin mahaifinsa a Mamre, a Kiriyat-arba, wato Hebron ke nan, inda Ibrahim da Ishaku suka yi baƙunci.

28. Yanzu kuwa kwanakin Ishaku shekara ce ɗari da tamanin.

29. Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, 'ya'yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.

Karanta cikakken babi Far 35