Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 35:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan Allah ya tashi Sama ya bar shi a wurin da ya yi masa magana.

14. Sai Yakubu ya kafa al'amudin dutse a inda Allah ya yi masa magana, ya zuba masa sadaka ta sha, ya kuma zuba mai a bisansa.

15. Yakubu ya kira sunan wurin da Allah ya yi magana da shi, Betel.

16. Da suka tashi daga Betel, tun suna da 'yar rata da Efrata, sai lokaci ya yi da Rahila za ta haihu, amma ta sha wahala kafin ta haihu.

17. Sa'ad da take cikin naƙudarta, sai ungozoma ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”

18. Da tana suma, sai ta sa masa suna Ben-oni, amma mahaifinsa ya sa masa suna Biliyaminu.

19. Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato Baitalami.

20. Yakubu ya kafa al'amudi bisa kabarinta, al'amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.

21. Isra'ila ya ci gaba da tafiyarsa, ya kuwa kafa alfarwarsa daura da hasumiyar Eder.

Karanta cikakken babi Far 35