Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 31:36-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Yakubu ya husata, ya yi wa Laban faɗa, ya ce wa Laban, “Wane laifi na yi, mene ne zunubina da ka tsananta bina?

37. Ko da yake ka wawaka dukan kayayyakina, me ka samu na gumakanka a ciki? A tabbatar a nan yau a gaban dangina da danginka, su yanke shari'a tsakanina da kai.

38. Waɗannan shekaru ashirin da na yi tare da kai, tumakinka da awakinka ba su yi ɓari ba, ban kuwa ci ragunan garkenka ba.

39. Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna.

40. Abin da na zama ke nan, da rana na sha zafin rana, da dare kuwa na sha sanyi, ga rashin barci.

41. A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma.

42. Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”

43. Sa'an nan Laban ya amsa ya ce wa Yakubu, “'Ya'ya mata, 'ya'yana ne, 'ya'yansu kuma nawa ne, garkunan, garkunana ne, dukan abin da kake gani nawa ne. Amma me zan yi a wannan rana ta yau ga waɗannan 'ya'ya mata nawa, ko kuma ga 'ya'yan da suka haifa?

44. Zo mana mu ƙulla alkawari, da ni da kai, bari ya zama shaida tsakanina da kai.”

45. Saboda haka Yakubu ya ɗauki dutse ya kafa shi al'amudi.

46. Yakubu ya ce wa iyalinsa, “Ku tattara duwatsu.” Sai suka ɗauki duwatsu, suka tsiba, suka kuwa ci abinci kusa da tsibin.

47. Laban ya sa masa suna Yegar-sahaduta, amma Yakubu ya kira shi Galeyed.

48. Laban ya ce, “Wannan tsibi shaida ce tsakanina da kai yau.” Saboda haka ya sa wa wurin suna Galeyed.

Karanta cikakken babi Far 31