Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 30:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”

2. Fushin Yakubu ya yi ƙuna a kan Rahila, ya ce, “Ina daidai da Allah ne, wanda ya hana ki haihuwa?.”

3. Sai ta ce, “Ga kuyangata Bilha, ka shiga wurinta, domin ta haihu bisa gwiwoyina, domin ni ma in sami 'ya'ya ta wurinta.”

4. Don haka ta ba shi Bilha ta zama matarsa. Yakubu kuwa ya shiga wurinta.

5. Bilha kuwa ta yi ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa.

6. Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni, ya ji muryata, ya kuwa ba ni ɗa.” Saboda haka ta raɗa masa suna Dan.

7. Bilha, kuyangar Rahila, ta sāke yin ciki, ta haifa wa Yakubu ɗa na biyu.

8. Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da 'yar'uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali.

Karanta cikakken babi Far 30