Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 3:6-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci.

7. Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.

8. Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la'asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar.

9. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”

10. Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”

11. Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”

12. Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci.”

13. Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?”Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”

14. Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la'ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka.

15. Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”

16. Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”

17. Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.

Karanta cikakken babi Far 3