Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 29:24-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. (Laban ya ba 'yarsa Lai'atu Zilfa ta zama kuyangarta).

25. Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”

26. Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin 'yar fari.

27. Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa'an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.”

28. Yakubu kuwa ya yi haka ɗin, ya cikasa makon, sa'an nan Laban ya aurar masa da 'yarsa Rahila.

29. (Laban ya ba 'yarsa Rahila Bilha, kuyangarsa, ta zama kuyangarta).

30. Sai Yakubu ya shiga wurin Rahila, amma ya fi ƙaunar Rahila da Lai'atu. Ya yi wa Laban barantaka waɗansu shekara bakwai kuma.

31. Sa'ad da Ubangiji ya ga ana ƙin Lai'atu, ya buɗe mahaifarta, amma Rahila bakarariya ce.

32. Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”

33. Ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Saboda Ubangiji ya ji ana ƙina ya ba ni wannan ɗa kuma,” ta kuwa raɗa masa suna Saminu.

34. Sai kuma ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “Yanzu, a wannan karo mijina zai shaƙu da ni , domin na haifa masa 'ya'ya uku maza.” Saboda haka ta raɗa masa suna Lawi.

35. Har yanzu kuwa ta sāke yin ciki, ta haifi ɗa, ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta raɗa masa suna Yahuza. Daga nan sai ta daina haihuwa.

Karanta cikakken babi Far 29