Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 29:15-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Laban kuwa ya ce wa Yakubu, “Don kana dangina, za ka yi mini barantaka a banza? Ka faɗa mini, nawa zan biya ka?”

16. Laban dai yana da 'ya'ya mata biyu, sunan babbar Lai'atu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.

17. Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.

18. Yakubu ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce wa Laban, “Zan yi maka barantaka shekara bakwai domin 'yarka Rahila.”

19. Laban ya ce, “Gara in ba ka ita da in ba wani dabam, zauna tare da ni.”

20. Saboda haka, ya yi barantaka shekara bakwai domin Rahila, amma a ganinsa kamar 'yan kwanaki ne saboda ƙaunar da yake mata.

21. Yakubu ya ce wa Laban, “Ba ni matata domin in shiga wurinta, domin lokacin da muka shirya ya cika.”

22. Sai Laban ya tattara mutanen wurin duka, ya yi biki.

23. Amma da maraice, ya ɗauki 'yarsa Lai'atu ya kawo ta wurin Yakubu, Yakubu ya shiga a wurinta.

24. (Laban ya ba 'yarsa Lai'atu Zilfa ta zama kuyangarta).

25. Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”

26. Laban ya ce, “A nan wurinmu ba a yin haka, a aurar da ƙarama kafin 'yar fari.

27. Ka jira, bayan kwana bakwai na lokacin auren sun wuce, sa'an nan za mu ba ka Rahila saboda barantakar da za ka yi mini shekara bakwai nan gaba.”

Karanta cikakken babi Far 29