Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 29:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya.

2. Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.

3. A sa'ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa'an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.

4. Yakubu ya ce musu, “'Yan'uwana, daga ina kuka fito?”Suka ce, “Daga Haran muke.”

5. Sai ya ce musu, “Kun san Laban ɗan Nahor?”Suka ce, “Mun san shi.”

6. Ya ce musu, “Lafiyarsa ƙalau?”Suka ce, “I, lafiya ƙalau yake, ga ma Rahila 'yarsa, tana zuwa da bisashensa!”

7. Ya ce, “Ga shi kuwa, da sauran rana da yawa, lokacin tattaruwar dabbobi bai yi ba, me zai hana ku shayar da tumakin, ku sāke kai su wurin kiwo?”

8. Amma suka ce, “Ba za mu iya ba, sai sauran garkunan duka sun taru, sa'an nan a kawar da dutsen daga bakin rijiyar, sa'an nan mu shayar da garkuna.”

9. Kafin ya rufe baki, sai ga Rahila ta zo da bisashen mahaifinta, gama ita take kiwonsu.

10. Sa'ad da Yakubu ya ga Rahila, 'yar Laban kawunsa, da bisashen, sai Yakubu ya hau ya kawar da dutsen daga bakin rijiyar, ya shayar da garken Laban, kawunsa.

11. Yakubu kuwa ya sumbaci Rahila, ya fara kuka da ƙarfi.

12. Ya faɗa mata shi dangin mahaifinta ne, shi kuma ɗan Rifkatu ne, sai ta sheƙa ta faɗa wa mahaifinta.

Karanta cikakken babi Far 29