Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 27:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.”

14. Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so.

15. Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su,

16. fatun 'yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi.

17. Sai ta bai wa ɗanta, Yakubu, abinci mai daɗin ci da gurasar da ta shirya.

18. Ya kuwa shiga wurin mahaifinsa, ya ce, “Baba.”Mahaifin ya ce, “Ga ni, wane ne kai, ya ɗana?”

19. Yakubu ya ce wa mahaifinsa, “Ni ne Isuwa ɗan farinka. Na yi yadda ka faɗa mini, in ka yarda ka tashi ka ci naman da na harbo, domin ka sa mini albarka.”

20. Amma Ishaku ya ce wa ɗansa, “Ƙaƙa aka yi ka same shi da sauri haka, ɗana?”Sai ya amsa, “Domin Ubangiji, Allahnka, ya ba ni sa'a.”

21. Ishaku kuwa ya ce wa Yakubu, “Matso kusa in ka yarda, don in lallaluba ka, ɗana, domin in hakikance ko kai ne ɗana Isuwa, ko babu.”

22. Saboda haka Yakubu ya matsa kusa da Ishaku mahaifinsa, sai ya lallaluba shi, ya ce, “Murya, muryar Yakubu ce, amma hannuwa, hannuwan Isuwa ne.”

Karanta cikakken babi Far 27