Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 27:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Lokacin da Ishaku ya tsufa, idanunsa kuma suka yi duhu har ba ya iya gani, sai ya kira Isuwa babban ɗansa, ya ce masa, “Ɗana!”Sai ya amsa, “Ga ni nan.”

2. Ishaku ya ce, “Ga shi, na tsufa, ban san ranar rasuwata ba.

3. Yanzu fa, ka ɗauki makamanka, da kwarinka da bakanka, ka tafi jeji ka farauto mini nama,

4. ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”

5. Rifkatu kuwa tana ji lokacin da Ishaku yake magana da ɗansa Isuwa. Don haka, sa'ad da Isuwa ya tafi jeji garin ya farauto nama ya kawo,

6. sai Rifkatu ta ce wa ɗanta Yakubu, “Na ji mahaifinka ya yi magana da ɗan'uwanka Isuwa, ya ce,

7. ‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.’

8. Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka.

9. Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so.

10. Kai kuwa ka kai wa mahaifinka, ya ci, domin ya sa maka albarka kafin ya rasu.”

11. Amma Yakubu ya ce wa Rifkatu mahaifiyarsa, “Ga shi fa, ɗan'uwana Isuwa gargasa ne, ni kuwa mai sulɓi ne.

12. Watakila, baba zai lallaluba ni, zai kuwa ce, ruɗinsa nake yi, in kuwa jawo wa kaina la'ana maimakon albarka.”

13. Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.”

14. Ya tafi ya kamo su, ya kawo su ga mahaifiyarsa, mahaifiyarsa kuwa ta shirya abinci mai daɗi irin wanda mahaifinsa yake so.

15. Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su,

16. fatun 'yan awakin kuwa ta naɗe wa hannuwansa, da sashen dokin wuyansa mai sulɓi.

Karanta cikakken babi Far 27