Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 26:20-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa,“Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta.

21. Suka haƙa wata rijiya, suka yi jayayya a kan wannan kuma, ya sa mata suna Sitna.

22. Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.”

23. Daga nan ya haura zuwa Biyer-sheba.

24. Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”

25. Ishaku ya gina bagade a wurin ya kira bisa sunan Ubangiji, a can kuwa ya kafa alfarwarsa. A can ne kuma barorin Ishaku suka haƙa rijiya.

26. Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku.

27. Sai Ishaku ya ce musu, “Me yake tafe da ku zuwa gare ni, ga shi kun ƙi ni, kun kuma kore ni nesa da ku?”

28. Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai,

29. cewa ba za ka cuce mu ba, daidai kamar yadda ba mu taɓe ka ba, ba mu yi maka kome ba sai alheri, muka kuwa sallame ka cikin salama. Yanzu, kai albarkatacce ne na Ubangiji.”

30. Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha.

31. Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama.

32. Ya zama kuwa a wannan rana, barorin Ishaku suka zo suka faɗa masa zancen rijiyar da suka haƙa, suka ce masa, “Mun sami ruwa.”

33. Ya sa mata suna Sheba, domin haka har yau sunan birnin Biyer-sheba.

34. Sa'ad da Isuwa yake da shekara arba'in, ya auro Judit, 'yar Biyeri Bahitte, da Basemat 'yar Elon Bahitte,

35. suka baƙanta wa Ishaku da Rifkatu rai.

Karanta cikakken babi Far 26