Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 26:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.

14. Da yake ya yi ta arzuta da garken tumaki, da na shanu, da iyali masu yawa, Filistiyawa suka ji ƙyashinsa.

15. Saboda haka, Filistiyawa don kishi sai suka ciccike rijiyoyin da ƙasa, waɗanda barorin mahaifinsa, Ibrahim, suka haƙa tun Ibrahim yana da rai.

16. Abimelek kuwa ya ce wa Ishaku, “Fita daga cikinmu, gama ka fi ƙarfinmu.”

17. Don haka Ishaku ya bar wurin, ya yi zango cikin kwarin Gerar, ya yi zamansa a can.

18. Sai Ishaku ya sāke haƙa rijiyoyi waɗanda dā aka haƙa a zamanin Ibrahim mahaifinsa, gama Filistiyawa sun tattoshe su bayan rasuwar Ibrahim. Ishaku kuma ya sa wa rijiyoyin sunayen da mahaifinsa ya sa musu.

19. Amma sa'ad da barorin Ishaku suka haƙa rijiya a kwarin, sai suka tarar da idon ruwa.

20. Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa,“Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta.

21. Suka haƙa wata rijiya, suka yi jayayya a kan wannan kuma, ya sa mata suna Sitna.

22. Sai ya zakuɗa daga nan ya haƙa wata rijiya kuma, amma ba su yi jayayya a kan wannan ba, don haka ya sa mata suna Rehobot, yana cewa, “Gama yanzu Ubangiji ya yalwata mana, za mu hayayyafa a ƙasa.”

23. Daga nan ya haura zuwa Biyer-sheba.

Karanta cikakken babi Far 26