Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 25:9-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ishaku da Isma'ilu 'ya'yansa suka binne shi a kogon Makfela a saurar Efron ɗan Zohar Bahitte, gabashin Mamre,

10. wato saurar da Ibrahim ya saya a wurin Hittiyawa. Can ne aka binne Ibrahim gab da Saratu matarsa.

11. Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.

12. Waɗannan su ne zuriyar Isma'ilu ɗan Ibrahim, wanda Hajaratu Bamasariya, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

13. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma'ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam,

14. da Mishma, da Duma, da Massa,

15. da Hadad, da Tema, da Yetur, da Nafish, da Kedema.

16. Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, bisa ga ƙauyukansu da zangonsu, hakimai goma sha biyu, bisa ga kabilansu.

17. Waɗannan su ne shekarun Isma'ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.

18. Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.

19. Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim, Ibrahim ya haifi Ishaku.

20. Ishaku yana da shekara arba'in sa'ad da ya auri Rifkatu, 'yar Betuwel Ba'aramiye daga Fadan-aram 'yar'uwar Laban Ba'aramiye.

Karanta cikakken babi Far 25