Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 24:12-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim.

13. Ga shi kuwa, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ga kuma 'yan matan mutanen birnin suna fitowa garin ɗibar ruwa.

14. Bari budurwar da zan ce wa, ‘Ina roƙo, ki sauke tulunki domin in sha,’ wadda za ta ce, ‘Sha, zan kuma shayar da raƙumanka,’ bari ta zama ita ce wadda ka zaɓa wa baranka Ishaku. Ta haka zan sani ka nuna madawwamiyar ƙaunarka ga maigidana.”

15. Kafin ya rufe baki, sai ga Rifkatu wadda aka haifa wa Betuwel ɗan Milka, matar Nahor ɗan'uwan Ibrahim, ta fito da tulun ruwanta a bisa kafaɗarta.

16. Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro.

17. Sai baran ya tarye ta a guje, ya ce, “Roƙo nake, ki ba ni ruwa kaɗan daga cikin tulunki in sha.”

18. Ta ce, “Sha, ya shugabana.” Nan da nan ta sauke tulunta ta riƙe a hannunta, ta ba shi ya sha.

19. Sa'ad da ta gama shayar da shi, ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka kuma, har su gama sha.”

20. Sai nan da nan ta bulbule tulunta a cikin kwami, ta sāke sheƙawa a guje zuwa rijiyar, ta kuwa ɗebo wa raƙumansa duka.

21. Mutumin kuwa ya zura mata ido, shiru, yana so ya sani ko Allah ya arzuta tafiyarsa, ko kuwa babu?

22. Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,

23. ya ce, “Ki faɗa mini ke 'yar gidan wace ce? Akwai masauki a gidan mahaifinki inda za mu sauka?”

24. Sai ta ce masa, “Ni 'yar Betuwel ce ɗan Milka wanda ta haifa wa Nahor.”

25. Ta ƙara da cewa, “Muna da isasshen baro da harawa duka, da kuma masauki.”

26. Mutumin ya yi ruku'u ya yi wa Ubangiji sujada,

27. ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa ga maigidana ba. Ubangiji ya bi da ni har zuwa gidan ɗan'uwan maigidana.”

28. Budurwar ta sheƙa a guje zuwa gida wurin mahaifiyarta ta faɗi waɗannan abubuwa.

Karanta cikakken babi Far 24