Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 22:14-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sai Ibrahim ya sa wa wurin suna, “Ubangiji zai tanada,” kamar yadda ake faɗa har yau, “A bisa kan dutsen Ubangiji, za a tanada.”

15. Mala'ikan Ubangiji kuma ya sāke kiran Ibrahim, kira na biyu daga sama,

16. ya ce, “Na riga na rantse da zatina, tun da ka yi wannan, ba ka kuwa ƙi ba da tilon ɗanka ba,

17. hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,

18. ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.”

19. Sai Ibrahim ya koma wurin samarinsa. Suka tashi suka tafi Biyer-sheba tare. Ibrahim ya yi zamansa a Biyer-sheba.

20. Ana nan bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Ibrahim, “Ga shi, Milka ta haifa wa ɗan'uwanka Nahor, 'ya'ya.

21. Uz ɗan fari, da Buz ɗan'uwansa, da Kemuwel mahaifin Aram,

Karanta cikakken babi Far 22