Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 20:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi zuwa wajen karkarar Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. A lokacin da Ibrahim yake baƙunci a Gerar,

2. ya ce, matarsa Saratu 'yar'uwarsa ce. Sai Abimelek Sarkin Gerar ya aika, aka ɗauko masa Saratu.

3. Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.”

4. Abimelek bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ubangiji, za ka hallaka marar laifi?

5. Ba shi ya faɗa mini, ‘Ita 'yar'uwata ce’ ba? Ba ita kanta kuma ta ce, ‘Shi ɗan'uwana ne’ ba? Cikin mutunci da kyakkyawan nufi na aikata wannan.”

6. Allah ya ce masa cikin mafarki, “I, na sani ka yi wannan cikin mutunci, ai, ni na hana ka ka aikata zunubin, don haka ban yarda maka ka shafe ta ba.

Karanta cikakken babi Far 20