Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 19:29-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Amma sa'ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.

30. Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da 'ya'yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da 'ya'yansa biyu mata.

31. Sai 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Mahaifinmu ya tsufa, ba wanda zai aure mu yadda aka saba yi ko'ina a duniya.

32. Zo dai, mu sa mahaifinmu ya sha ruwan inabi, sa'an nan sai mu kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”

33. Sai suka sa mahaifinsu ya sha ruwan inabi. Da daren nan kuwa 'yar farin ta shiga ta kwana da mahaifinta, shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.

34. Kashegari kuma, 'yar farin ta ce wa ƙaramar, “Ga shi, daren jiya na kwana da mahaifina, bari daren yau kuma, mu sa shi ya sha ruwan inabi, ke ma sai ki shiga ki kwana da shi, domin kada zuriyar mahaifinmu ta ƙare.”

35. Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.

36. Haka nan kuwa, 'ya'yan Lutu biyu ɗin nan suka sami ciki daga mahaifinsu.

37. Ta farin, ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Mowab. Shi ne asalin Mowabawa har yau.

38. Ƙaramar kuma ta haifi ɗa namiji, ta sa masa suna Benammi, shi ne asalin Ammonawa har yau.

Karanta cikakken babi Far 19