Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 19:11-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai suka bugi mutanen da suke ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu suna laluba inda ƙofa take.

12. Mutanen suka ce wa Lutu, “Kana da wani naka a nan? Ko surukai, ko 'ya'ya mata da maza, ko dai kome naka da yake cikin birnin? Fito da su daga wurin,

13. gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.”

14. Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.

15. Sa'ad da safiya ta gabato, mala'ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da 'ya'yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.”

16. Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na 'ya'yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin.

17. Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”

18. Sai Lutu ya ce musu, “A'a, ba haka ba ne iyayengijina,

19. ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu.

20. Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”

21. Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba.

22. Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.

23. Da hantsi Lutu ya isa Zowar.

Karanta cikakken babi Far 19