Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 18:18-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ga shi kuwa, Ibrahim zai ƙasaita ya zama al'umma mai iko, sauran al'umman duniya duka za su sami albarka ta dalilinsa.

19. Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.

20. Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai,

21. zan sauka in gani ko sun aikata kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.”

22. Sa'an nan mutanen suka juya daga nan, suka nufi Saduma, amma Ibrahim ya tsaya a gaban Ubangiji.

23. Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun?

24. Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba?

25. Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”

26. Sai Ubangiji ya ce, “In na sami adalai hamsin a cikin birnin Saduma, zan yafe wa dukan wurin sabili da su.”

27. Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.

28. Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?”Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba'in da biyar a wurin.”

29. Ya kuma sāke yin masa magana, ya ce, “Da a ce za a sami arba'in a wurin fa?”Ya amsa ya ce, “Sabili da arba'in ɗin ba zan yi ba.”

30. Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan yi magana. Da a ce za a sami talatin a wurin fa?”Ya amsa, “Ba zan yi ba, in na sami talatin a wurin.”

31. Ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji. Da a ce za a sami ashirin a wurin fa?”Ya amsa ya ce, “Sabili da ashirin ɗin ba zan hallaka shi ba.”

32. Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan sāke yin magana, sau ɗayan nan kaɗai. Da a ce za a sami goma a wurin fa?”Ya amsa ya ce, “Sabili da goma ɗin ba zan hallaka shi ba.”

33. Ubangiji kuwa ya yi tafiyarsa, bayan ya gama magana da Ibrahim. Ibrahim kuwa ya koma gida.

Karanta cikakken babi Far 18