Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 15:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai ga maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Mutumin nan, ba shi zai gāje ka ba, ɗan cikinka shi zai gāje ka.”

5. Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”

6. Ya amince da Ubangiji, Ubangiji kuwa ya lasafta wannan adalci ne a gare shi.

7. Ubangiji kuma ya ce masa, “Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ka daga Ur ta Kaldiyawa, don in ba ka wannan ƙasa ka gāje ta.”

8. Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, yaya zan mallake ta?”

9. Ya ce masa, “Kawo mini karsana bana uku, da burguma bana uku, da rago bana uku, da hazbiya da ɗan tattabara.”

10. Ya kawo masa waɗannan abu duka, ya yanyanka su ya tsattsaga su a tsaka, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba.

11. Sa'ad da tsuntsaye masu cin nama suke sauka bisansu sai Abram ya kore su.

Karanta cikakken babi Far 15