Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Far 12:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ana nan sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka fita daga ƙasarka, da danginka, da gidan mahaifinka zuwa ƙasar da zan nuna maka.

2. Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.

3. Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”

4. Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran.

5. Abram kuwa ya ɗauki matarsa Saraya da Lutu, ɗan ɗan'uwansa, da dukan dukiyarsu, da dukan mallakarsu waɗanda suka tattara a Haran.Sa'ad da suka kai ƙasar Kan'ana,

6. Abram ya ratsa ƙasar zuwa Shekem, wurin itacen oak na More. A lokacin nan Kan'aniyawa suke a ƙasar.

7. Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.

8. Ya zakuɗa daga nan zuwa dutsen da yake gabashin Betel, ya kafa alfarwarsa, Betel tana yamma, Ai tana gabas, a nan ya gina wa Ubangiji bagade, ya kira bisa sunan Ubangiji.

9. Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.

10. A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.

Karanta cikakken babi Far 12