Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 7:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. “Da wannan kuɗi ne za ka himmatu, ka sayi bijimai, da raguna, da 'yan raguna, da hadayunsu na gari, da na sha. Za ka miƙa su a bisa bagaden Haikalin Allah da yake a Urushalima.

18. Duk abin da kai da 'yan'uwanka kuka ga ya dace ku yi, sai ku yi shi da sauran azurfa da zinariya bisa ga nufin Allahnku.

19. Kwanonin da aka ba ka domin hidima a Haikalin Allah, sai ka ajiye su a gaban Allah a Urushalima.

20. Dukan abin da ake bukata domin Haikalin Allah, abin nan kuwa ya kamata a yi shi, sai ka yi shi da kuɗin baitulmalin sarki.

21. “Ni, sarki Artashate, ina umartar kowane ma'aji na Yammacin Kogin Yufiretis, cewa duk abin da Ezra, firist, masanin dokokin Allah na Sama, zai bukata a gare ka, sai ka himmatu ka yi.

22. Sai ku ba shi abin da ya kai talanti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari ta ruwan inabi, mai kuma garwa ɗari. Gishiri kuwa a bayar da yawa, kada a iyakance.

23. Dukan abin da Allah na Sama ya umarta, sai a yi shi sosai domin Haikalin Allah na Sama, domin kada ya yi fushi da mulkin sarki da 'ya'yansa.

24. Muna kuma sanar da ku, cewa ba daidai ba ne ku karɓi haraji, da kuɗin shiga da fita, daga wurin firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da masu lura da Haikali, da ma'aikatan wannan Haikali na Allah.

25. “Kai kuma, Ezra, bisa ga hikimar da Allahnka ya ba ka, sai ka naɗa mahukunta da alƙalai waɗanda za su yi wa mutanen da suke a lardin Yammacin Kogi shari'a, wato dukan waɗanda suka san shari'a. Waɗanda ba su san shari'a ba kuwa, sai ka koya musu.

26. Duk wanda bai yi biyayya da shari'ar Allahnka ba, ko shari'ar sarki, sai a yi masa hukunci mai tsanani, ko na mutuwa, ko na kora, ko na ƙwace dukiyarsa, ko na kurkuku.”

27. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na kakanninmu, wanda ya sa a zuciyar sarki ya ƙawata Haikalin Ubangijin da yake a Urushalima.

28. Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a wurin sarki, da 'yan majalisarsa, da manyan ma'aikatansa. Na sami ƙarfin hali, gama Ubangiji Allahna yana tare da ni. Sai na tattara manyan mutane na Isra'ila don mu tafi tare.

Karanta cikakken babi Ezra 7