Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 7:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ta ce, “Daga Artashate, sarkin sarakuna, zuwa ga Ezra firist, masanin shari'ar Allah na Sama.

13. “Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra'ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.

14. Gama sarki ne da 'yan majalisarsa guda bakwai suka aike ka don ka san irin zaman mutanen Yahuza da na Urushalima game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka,

15. domin kuma ka ba da azurfa da zinariya waɗanda sarki da 'yan majalisarsa suka ba Allah na Isra'ila da yardar ransu, wato Allah wanda Haikalinsa yake a Urushalima,

16. da kuma azurfa da zinariya da za ka samu a dukan lardin Babila tare da hadayu na yardar rai daga mutane da firistoci, hadayun da suka yi wa'adi su bayar da yardar ransu domin Haikalin Allahnsu, da yake a Urushalima.

17. “Da wannan kuɗi ne za ka himmatu, ka sayi bijimai, da raguna, da 'yan raguna, da hadayunsu na gari, da na sha. Za ka miƙa su a bisa bagaden Haikalin Allah da yake a Urushalima.

18. Duk abin da kai da 'yan'uwanka kuka ga ya dace ku yi, sai ku yi shi da sauran azurfa da zinariya bisa ga nufin Allahnku.

19. Kwanonin da aka ba ka domin hidima a Haikalin Allah, sai ka ajiye su a gaban Allah a Urushalima.

20. Dukan abin da ake bukata domin Haikalin Allah, abin nan kuwa ya kamata a yi shi, sai ka yi shi da kuɗin baitulmalin sarki.

21. “Ni, sarki Artashate, ina umartar kowane ma'aji na Yammacin Kogin Yufiretis, cewa duk abin da Ezra, firist, masanin dokokin Allah na Sama, zai bukata a gare ka, sai ka himmatu ka yi.

22. Sai ku ba shi abin da ya kai talanti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari ta ruwan inabi, mai kuma garwa ɗari. Gishiri kuwa a bayar da yawa, kada a iyakance.

23. Dukan abin da Allah na Sama ya umarta, sai a yi shi sosai domin Haikalin Allah na Sama, domin kada ya yi fushi da mulkin sarki da 'ya'yansa.

Karanta cikakken babi Ezra 7