Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 9:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai na ji Allah ya yi kira da babbar murya, ya ce, “Ku matso kusa, ku masu hukunta wa birnin, kowa ya zo da makaminsa na hallakarwa a hannu.”

2. Sai ga mutum shida sun taho daga wajen ƙofa wadda take daga bisa wadda ta fuskanci arewa. Kowa yana da makaminsa na kisa a hannu. Tare da su kuma akwai wani mutum saye da rigar lilin, yana kuma rataye da gafaka. Sai suka tafi suka tsaya a gefen bagaden tagulla.

3. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tashi daga kan siffar kerubobi inda take zaune zuwa bakin ƙofar Haikalin. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda yake rataye da gafaka.

4. Ya ce masa, “Ka ratsa cikin birni, wato Urushalima, ka sa shaida a goshin mutanen da suke ajiyar zuciya, suna damuwa saboda dukan abubuwa masu banƙyama waɗanda ake aikatawa a birnin.”

5. Na kuma ji ya ce wa sauran, “Ku bi shi, ku ratsa cikin birnin, ku kashe, kada ku yafe, kada kuwa ku ji tausayi.

6. Ku kashe tsofaffi, da samari, da 'yan mata, da ƙananan yara, da mata, amma kada ku taɓa wanda yake da shaida. Sai ku fara a Haikalina.” Suka kuwa fara da dattawan da suke a gaban Haikalin.

Karanta cikakken babi Ez 9