Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 8:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kan rana ta biyar ga wata na shida a shekara ta shida ta zaman talala, sa'ad da nake zaune a gidana, dattawan Yahuza kuma suna zaune a gabana, sai ikon Ubangiji Allah ya sauka a kaina.

2. Da na duba, sai ga siffa wadda dake da kamannin mutum. Daga kwankwason siffar zuwa ƙasa yana da kamannin wuta, daga kwankwason kuma zuwa sama yana da haske kamar na tagulla.

3. Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda take fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.

4. Sai ga ɗaukakar Allah na Isra'ila a wurin, kamar wahayin da na gani a fili.

5. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗaga idanunka, ka duba wajen arewa.” Na kuwa ɗaga idanuna wajen arewa, na kuma ga siffa ta tsokano kishi a mashigin ƙofar bagade na wajen arewa.

6. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ga abin da suke yi, abubuwa masu banƙyama da mutanen Isra'ila suke yi a nan don su kore ni nesa da Haikalina? Ai, za ka ga abubuwa masu banƙyama da suka fi haka.”

7. Ya kuma kai ni ƙofar shirayi. Sa'ad da na duba, sai ga wani rami a bangon.

8. Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka haƙa bangon.” Da na haƙa bangon, sai ga ƙofa.

9. Ya ce, mini, “Ka shiga ka ga abubuwan banƙyama da suke aikatawa a nan.”

Karanta cikakken babi Ez 8