Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 47:16-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. da Hamat, da Berota, da Sibrayim, wadda take a iyakar tsakanin Dimashƙu da Hamat, har zuwa Hazer-hattikon wadda take iyakar Hauran.

17. Iyakar za ta bi daga teku zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu. Iyakar Hamat tana wajen arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.

18. “A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra'ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.

19. “A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

20. “A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

21. “Za ku kuwa raba ƙasar a tsakaninku bisa ga kabilan Isra'ila.

22. Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila,

23. a cikin kabilar da baƙon yake zaune, nan ne za ku ba shi nasa gādo, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 47