Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 47:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Za ku raba daidai, gama na rantse zan ba kakanninku wannan ƙasa, za ta kuwa zama gādonku.

15. “A wajen arewa, iyakar za ta kama daga Bahar Rum, ta bi ta hanyar Hetlon zuwa Zedad,

16. da Hamat, da Berota, da Sibrayim, wadda take a iyakar tsakanin Dimashƙu da Hamat, har zuwa Hazer-hattikon wadda take iyakar Hauran.

17. Iyakar za ta bi daga teku zuwa Hazar-enan wadda take iyakar Dimashƙu. Iyakar Hamat tana wajen arewa. Wannan ita ce iyakar a wajen arewa.

18. “A wajen gabas, iyakar za ta kama daga Hazar-enan tsakanin Hauran da Dimashƙu, ta bi ta Urdun tsakanin Gileyad da ƙasar Isra'ila zuwa tekun gabas har zuwa Tamar. Wannan ita ce iyakar a wajen gabas.

19. “A wajen kudu, iyakar za ta kama daga Tamar har zuwa ruwan Meribakadesh, ta bi ta rafin Masar zuwa Bahar Rum. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

20. “A wajen yamma, Bahar Rum shi ne iyakar zuwa ƙofar Hamat. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

21. “Za ku kuwa raba ƙasar a tsakaninku bisa ga kabilan Isra'ila.

22. Za ku raba ƙasar gādo a tsakaninku da baƙin da suke zaune tare da ku, waɗanda suka haifi 'ya'ya a cikinku. Za su zama kamar 'ya'yan Isra'ila haifaffu na gida. Za a ba su gādo tare da kabilan Isra'ila,

23. a cikin kabilar da baƙon yake zaune, nan ne za ku ba shi nasa gādo, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 47