Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 42:15-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sa'ad da ya gama auna cikin Haikalin, ya fito da ni ta ƙofar gabas, sa'an nan ya auna filin da yake kewaye da Haikalin.

16. Ya auna kusurwar gabas da karan awo, kamu ɗari biyar.

17. Sai kuma ya auna kusurwar arewa, kamu ɗari biyar.

18. Kusurwar kudu kamu ɗari biyar.

19. Kusurwar yamma, ita ma kamu ɗari biyar.

20. Ya auna dukan kusurwoyi huɗu. Filin yana kewaye da katanga mai tsawo kamu ɗari biyar ne, fāɗi kuma kamu ɗari biyar don ya raba Wuri Mai Tsarki da sauran wurin.

Karanta cikakken babi Ez 42