Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 42:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan ya kai ni a farfajiya da yake waje, ya kuma kai ni ɗakunan da yake kusa da farfajiyar Haikali, daura da ginin da yake wajen arewa.

2. Tsawon ginin da yake wajen gefen arewa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu hamsin.

3. A gaban kamu ashirin na farfajiyar da yake can ciki, da kuma a gaban daɓen farfajiyar da take waje, akwai jerin ɗakuna hawa uku uku.

4. A gaban ɗakunan akwai hanya mai faɗin kamu goma, tsawonta kuwa kamu ɗari. Ƙofofinsu suna fuskantar arewa.

5. Ɗakunan da suke a hawa na uku ba su da fāɗi, gama hanyar benen ya cinye wuri fiye da ɗakunan da suke a hawa na ƙasa da na tsakiya.

6. Ɗakunan suna da hawa uku, amma ba su da ginshiƙai kamar na farfajiyar da suke waje. Saboda haka ɗakunan da suke a hawa na uku ba su kai girman waɗanda suke a hawa na ƙasa da na tsakiya ba.

7. Tsawon katangar waje wadda take gefen ɗakunan farfajiyar waje wanda yake daura da ɗakunan kamu hamsin ne.

8. Tsawon ɗakunan da suke fuskantar farfajiyar waje kamu hamsin ne. Waɗanda suke fuskantar Haikalin kuwa tsawonsu kamu ɗari ne.

Karanta cikakken babi Ez 42