Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 39:13-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Dukan jama'ar ƙasar za su yi aikin binnewar, zai zama daraja a gare su a ranar da zan bayyana ɗaukakata, ni Ubangiji Allah na faɗa.

14. A ƙarshen wata bakwai ɗin za su keɓe waɗansu mutane domin su bi ko'ina cikin ƙasar, su binne sauran gawawwakin da suka ragu a ƙasar don su tsabtace ta.

15. Sa'ad da waɗannan suke bibiyawa a cikin ƙasar, duk wanda ya ga ƙashin mutum, sai ya kafa wata alama kusa da ƙashin don masu binnewa su gani, su ɗauka, su binne a Kwarin Rundunar Gog.

16. Akwai gari a wurin, za a sa masa suna Hamona, wato runduna. Ta haka za su tsabtace ƙasar.

17. “Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko'ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra'ila. Za su ci nama su kuma sha jini.

18. Za su ci naman mutane masu iko, su sha jinin shugabannin duniya, waɗanda aka kashe kamar yadda ake yanka raguna, da 'yan tumaki, da awaki, da bijimai, da dukan turkakkun Bashan.

19. Za su ci kitse, har su gundura, su sha jini kuma, har su bugu a idin da nake shirya musu.

20. Za a ƙosar da su da naman dawakai, da na mahayansu da na mutane masu iko, da na dukan mayaƙa, ni Ubangiji na faɗa.”

21. “Zan nuna ɗaukakata a cikin al'ummai, dukan al'ummai kuwa za su ga hukuncin da na yi da ikon da na nuna kansu.

Karanta cikakken babi Ez 39