Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 34:17-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. “Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Ku kuma garkena, zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin rago da bunsuru.

18. A ganinku abu mai kyau ne, bayan da kun yi kiwo a makiyaya mai kyau, sa'an nan ku tattake sauran makiyayar da ƙafafunku? Sa'ad da kuka sha ruwa mai kyau, sai kuma ku gurɓata sauran da ƙafafunku?

19. Dole ne tumakina su ci abin da kuka tattake da ƙafafunku, su kuma sha abin da kuka gurɓata da ƙafafunku!’

20. “Saboda haka, ni, Ubangiji Allah, na ce, ‘Zan shara'anta tsakanin turkakkun tumaki da ramammu.

21. Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku, har kun watsar da su.

22. Zan ceci garken tumakina, ba za su ƙara zama ganima ba. Zan kuma shara'anta tsakanin tunkiya da tunkiya.

23. Zan sa musu makiyayi guda, wato bawana Dawuda. Zai yi kiwonsu, ya zama makiyayinsu.

24. Ni kuma, Ubangiji, zan zama Allahnsu. Bawana Dawuda kuwa zai zama sarkinsu.’ Ni Ubangiji na faɗa.

25. “Zan yi alkawarin salama da su. Zan kuwa kori namomin jeji daga ƙasar, domin tumakin su zauna lafiya a jeji, su kwana cikin kurmi.

26. Zan sa su, da wuraren da suke kewaye da tuduna dalilin samun albarka. Zan aiko da ruwan sama a lokacinsa, zai kuma zama ruwan albarka.

27. Itatuwan saura za su yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani. Za su zauna lafiya a ƙasarsu. Za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na karya karkiyarsu, na cece su daga hannun waɗanda suka bautar da su.

28. Ba za su ƙara zama ganimar al'ummai ba, namomin jejin ƙasar kuma ba za su cinye su ba. Za su yi zamansu lafiya, ba wanda zai tsorata su.

29. Zan ba su gonaki masu dausayi don kada yunwa ta ƙara far musu a ƙasar, kada kuma su ƙara shan zargi wurin sauran al'umma.

30. Za su sani ni Ubangiji Allahnsu, ina tare da su, mutanen Isra'ila kuwa su ne mutanena, ni Ubangiji Allah na faɗa.

31. “Ku tumakin makiyayata, ku mutane ne, ni kuwa Allahnku ne, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 34