Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 32:4-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Zan jefar da kai a tudu,A fili zan jefa ka.Zan sa tsuntsayen sararin sama su ɗira a kanka,Zan ƙosar da namomin jeji na dukan duniya da namanka.

5. Zan watsa namanka a kan duwatsu,In cika kwaruruka da gawarka.

6. Zan watsar da jininka a ƙasa da tuddai,Magudanan ruwa za su cika da jininka.

7. Sa'ad da na shafe ka, zan rufe sammai,In sa taurarinsu su duhunta,Zan sa girgije ya rufe rana,Wata kuma ba zai haskaka ba.

8. Dukan haskokin sama zan sa su zama duhu a gare ka,In sa ƙasarka ta duhunta, ni Ubangiji Allah na faɗa.’

9. “Zukatan al'ummai da yawa za su ɓaci, sa'ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba.

10. Al'ummai da yawa za su gigice saboda abin da zai same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa'ad da na kaɗa takobi a gabansu. A ranar faɗuwarka za su yi rawar jiki a kowane lokaci, kowa saboda ransa.”

11. Ubangiji Allah ya ce, “Takobin Sarkin Babila zai auko maka.

12. Zan sa ƙarfafan mutane masu bantsoro daga cikin al'ummai su kashe jama'arka da takuba.Za su wofinta girmankan Masar,Su kuma hallaka jama'arta.

13. Zan hallaka dukan dabbobinta da suke bakin ruwa,Ba ƙafar mutum ko ta dabba da za ta ƙara gurɓata ruwa.

14. Zan sa ruwansu ya yi garau,In sa kogunansu su malala kamar mai,Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15. Sa'ad da na mai da ƙasar Masar kufai,In raba ƙasar da abin da take cike da shi,Sa'ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta,Daga nan za su sani ni ne Ubangiji.

16. Wannan ita ce waƙar makokin. 'Yan matan al'ummai za su raira wa Masar da jama'arta duka, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

17. A rana ta goma sha biyar ga wata na fari, a shekara ta goma sha biyu, Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

Karanta cikakken babi Ez 32