Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 32:11-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ubangiji Allah ya ce, “Takobin Sarkin Babila zai auko maka.

12. Zan sa ƙarfafan mutane masu bantsoro daga cikin al'ummai su kashe jama'arka da takuba.Za su wofinta girmankan Masar,Su kuma hallaka jama'arta.

13. Zan hallaka dukan dabbobinta da suke bakin ruwa,Ba ƙafar mutum ko ta dabba da za ta ƙara gurɓata ruwa.

14. Zan sa ruwansu ya yi garau,In sa kogunansu su malala kamar mai,Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15. Sa'ad da na mai da ƙasar Masar kufai,In raba ƙasar da abin da take cike da shi,Sa'ad da na bugi dukan waɗanda suke cikinta,Daga nan za su sani ni ne Ubangiji.

16. Wannan ita ce waƙar makokin. 'Yan matan al'ummai za su raira wa Masar da jama'arta duka, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

17. A rana ta goma sha biyar ga wata na fari, a shekara ta goma sha biyu, Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

18. “Ɗan mutum, ka yi kuka saboda jama'ar Masar. Ka tura su tare da sauran al'umma zuwa lahira wurin waɗanda suka gangara zuwa cikin kabari.

19. Ka ce, ‘Su wa kika fi kyau? Ki gangara, ki kwanta tare da marasa imani.’

20. “An zare takobi don a kashe jama'ar Masar. Za su fāɗi a tsakiyar waɗanda aka kashe da takobi.

21. Manyan jarumawa daga lahira za su yi magana a kansu da mataimakansu, su ce, ‘Marasa imani waɗanda aka kashe da takobi, sun gangaro, ga su nan kwance shiru!’

22. “Assuriya tana can da dukan taron jama'arta. Kaburburansu suna kewaye da ita. An kashe dukansu da takobi.

23. An binne su a can ƙurewar lahira. Taron jama'arta suna kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Su ne suka haddasa tsoro a cikin ƙasar.

24. “Elam tana can da dukan jama'arta kewaye da kabarinta. An kashe dukansu da takobi. Sun gangara da rashin imaninsu zuwa lahira. Su ne suka haddasa tsoro a duniya. Sun sha kunyarsu tare da waɗanda suka gangara zuwa kabari.

Karanta cikakken babi Ez 32