Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 32:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A kan rana ta fari, ga watan goma sha biyu, a shekara ta goma sha biyu, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir'auna, Sarkin Masar, ka ce,‘Ka aza kanka kamar zaki a cikin al'ummai,Amma kai kada ne a cikin ruwa.Ka ɓullo cikin kogunanka,Ka gurɓata ruwa da ƙafafunka,Ka ƙazantar da kogunansu.’

3. Ubangiji Allah ya ce,‘Zan jefa taruna a kanka, a babban taron mutane,Zan jawo ka cikin taruna.

4. Zan jefar da kai a tudu,A fili zan jefa ka.Zan sa tsuntsayen sararin sama su ɗira a kanka,Zan ƙosar da namomin jeji na dukan duniya da namanka.

5. Zan watsa namanka a kan duwatsu,In cika kwaruruka da gawarka.

6. Zan watsar da jininka a ƙasa da tuddai,Magudanan ruwa za su cika da jininka.

7. Sa'ad da na shafe ka, zan rufe sammai,In sa taurarinsu su duhunta,Zan sa girgije ya rufe rana,Wata kuma ba zai haskaka ba.

8. Dukan haskokin sama zan sa su zama duhu a gare ka,In sa ƙasarka ta duhunta, ni Ubangiji Allah na faɗa.’

9. “Zukatan al'ummai da yawa za su ɓaci, sa'ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba.

10. Al'ummai da yawa za su gigice saboda abin da zai same ka, sarakunansu kuma za su yi rawar jiki saboda kai sa'ad da na kaɗa takobi a gabansu. A ranar faɗuwarka za su yi rawar jiki a kowane lokaci, kowa saboda ransa.”

Karanta cikakken babi Ez 32