Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 28:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. “Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Sarkin Taya, ka ce Ubangiji Allah ya ce,‘Kai cikakke ne, cike da hikima da jamali!

13. Kana cikin Aidan, gonar Allah.An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja,Tare da zinariya.Kana da molo da abin busa.A ranar da aka halicce kaSuna nan cikakku.

14. Na keɓe ka ka zama mala'ika mai tsaro,Kana bisa tsattsarkan dutsen Allah,Ka yi tafiya a tsakiyar duwatsu na wuta.

15. Daga ranar da aka halicce ka ba ka da laifi cikin al'amuranka,Sai ran da aka iske mugunta a cikinka.

16. A wurin yawan kasuwancinka,Ka yi rikici da yawa har ka yi zunubi.Don haka na jefar da kai daga dutsen AllahKamar ƙazantaccen abu.Na hallaka ka daga tsakiyar duwatsu na wuta,Kai mala'ikan tsaro.

17. Zuciyarka ta yi alfarma saboda kyanka,Ka lalatar da hikimarka ta wurin nuna darajar kanka.Na jefar da kai zuwa ƙasa,Na tone asirinka a gaban sarakuna don su kallace ka.

18. Saboda yawan muguntarka da rashin gaskiyarka cikin kasuwanci,Ka ƙazantar da tsarkakakkun wurarenka.Don haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka,Na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suka kallace ka.

19. Dukan waɗanda suka san ka a cikin al'ummaiZa su gigice saboda masifar da ta auko maka,Za ka zama barazana ga al'ummai,Ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.”’

20. Ubangiji ya yi magana da ni kuma, ya ce,

21. “Ɗan mutum, ka fuskanci Sidon, ka yi annabci a kanta.

22. Ka ce, Ubangiji Allah ya ce,‘Duba, ina gāba da ke, ya Sidon,Zan bayyana ikona a cikinki,Za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na hukunta ta,Na bayyana tsarkina a cikinta.

Karanta cikakken babi Ez 28