Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 25:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa, ka yi annabci a kansu.

3. Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,

4. domin haka zan bashe ku abin mallaka ga mutanen gabas. Za su kafa alfarwansu a cikinku, su zauna tare da ku. Za su ci amfanin gonakinku, su sha madararku.

5. Zan mai da Rabba makiyayar raƙuma, in mai da biranen Ammonawa garken awaki da tumaki. Sa'an nan ku sani ni ne Ubangiji Allah.”

6. Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila,

7. domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”

8. Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai,

9. saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab daga garuruwan da suke kan iyaka, waɗanda su ne darajarta, wato Bet-yeshimot, da Ba'al-meyon, da Kiriyatayim.

10. Zan bashe ta duk da Ammonawa su zama abin mallakar mutanen gabas, don kada um'ƙara tunawa da su a cikin al'ummai.

11. Zan hukunta Mowab, sa'an nan za ta sani ni ne Ubangiji.”

12. Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Edom ta ɗaukar wa kanta fansa a kan mutanen Yahuza, ta yi babban laifi da ta ɗaukar wa kanta fansa,

Karanta cikakken babi Ez 25