Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 23:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ohola ta yi karuwanci sa'ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa,

6. waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha'awa, suna bisa kan dawakansu.

7. Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

8. Ba ta bar karuwancinta ba, wanda ta yi tun tana a Masar, gama a lokacin 'yan matancinta mutane sun kwana da ita, sun rungumi ƙirjinta, suka biya kwaɗayinsu a kanta.

9. Domin haka na bashe ta a hannun kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

10. Waɗannan suka tsiraita ta, suka kama 'ya'yanta mata da maza, suka kashe ta da takobi. Sai ta zama abin karin magana a wurin mata sa'ad da aka hukunta ta.

11. “Ƙanwarta kuwa ta ga wannan, amma duk da haka ta fi ta lalacewa saboda kai da kawowa na karuwanci, wanda ya fi na 'yar uwarta muni.

12. Ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, a wurin masu mulki da manyan sojoji waɗanda suke saye da kayan yaƙi, suna bisa kan dawakai, dukansu samari ne masu bansha'awa.

13. Na ga ta ƙazantu. Dukansu biyu suka bi hanya ɗaya.

14. “Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a jikin bango, siffofin Kaldiyawa ne aka zāna da jan launi!

Karanta cikakken babi Ez 23