Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 23:38-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Ga kuma abin da suka yi mini, sun ƙazantar da Haikalina a ranar, sun kuma ɓata ranar Asabar ɗina.

39. Gama a ranar da suka kashe 'ya'yansu, suka miƙa su hadaya ga gumakansu, sai suka shiga Haikalina suka ƙazantar da shi. Abin da suka yi ke nan cikin Haidalina.

40. “Kun aiki manzo wurin mutanen da suke nesa su kuwa suka zo. Saboda su kun yi wanka, kun sa kwalli, kun ci ado.

41. Kun zauna a gado mai daraja, da tebur a shirye a gabansa. A kansa kuka ajiye turarena da maina.

42. A wurinta akwai hayaniyar taron mutane marasa kula, sai kuma aka kawo mutane irinsu, mashaya daga jeji. Suka sa mundaye a hannuwan matan, suka kuma sa kambi masu kyau a kawunansu.

43. Sai na yi magana a kanta, ita wadda ta ƙare ƙarfinta da yin zina, yanzu za su yi zina da ita da ta zama haka?

44. Suka shiga wurinta kamar yadda akan shiga wurin karuwa. Haka kuwa suka shiga wurin Ohola da Oholiba don su yi zina da su.

45. Amma adalai za su yanka musu hukunci irin wanda akan yi wa mata mazinata, da mata masu kisankai, gama su mazinata ne masu kisankai.

46. “Gama ni Ubangiji Allah na ce, a kawo rundunar soja ta yi yaƙi da su, don su firgita su, su washe su.

47. Rundunar za ta jajjefe su da duwatsu, ta sassare su da takuba. Za ta kuma kashe 'ya'yansu mata da maza, ta ƙone gidajensu.

48. Ta haka zan kawo ƙarshen lalata a cikin ƙasar domin dukan mata su sami faɗaka, kada su yi lalata kamar yadda kuka yi.

49. Za a hukunta ku saboda lalatarku, za ku sha hukunci saboda zunubin bautar gumaka, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.”

Karanta cikakken babi Ez 23