Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 23:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “Ƙanwarta kuwa ta ga wannan, amma duk da haka ta fi ta lalacewa saboda kai da kawowa na karuwanci, wanda ya fi na 'yar uwarta muni.

12. Ta yi ta kai da kawowa cikin Assuriyawa, a wurin masu mulki da manyan sojoji waɗanda suke saye da kayan yaƙi, suna bisa kan dawakai, dukansu samari ne masu bansha'awa.

13. Na ga ta ƙazantu. Dukansu biyu suka bi hanya ɗaya.

14. “Amma karuwancinta ya zarce. Ta ga an zāna mutane a jikin bango, siffofin Kaldiyawa ne aka zāna da jan launi!

15. Sun sha ɗamara a gindinsu, da rawuna a kansu suna kaɗawa filfil. Dukansu suna kama da jarumawa. Su siffofi suna kama da mutanen Babila na ƙasar Kaldiya.

16. Sa'ad da ta gan su, sai ta yi ta kai da kawowa a cikinsu. Ta aiki jakadu a wurinsu, wato a Kaldiya.

17. Sai Babilawa suka zo wurinta, a gadonta na nishaɗi, suka ƙazantar da ita ta wurin kwana da ita. Bayan da sun ƙazantar da ita, sai ta ji ƙyamarsu, ta rabu da su.

Karanta cikakken babi Ez 23