Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 23:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, akwai waɗansu mata biyu, uwarsu ɗaya.

3. Sun yi karuwanci a Masar, a lokacin 'yan matancinsu, aka rungumi mamansu da ƙirjinsu.

4. Sunan babbar Ohola, sunan ƙanwar kuwa Oholiba. Sun zama nawa, sun haifi 'ya'ya mata da maza. A kan sunayensu kuwa Ohola ita ce Samariya, Oholiba kuwa ita ce Urushalima.

5. Ohola ta yi karuwanci sa'ad da take zamana. Ta yi ta kai da kawowa a tsakanin kwartayenta, Assuriyawa,

6. waɗanda suke saye da shunayya, su masu mulki da manyan sojoji, dukansu samari ne masu bansha'awa, suna bisa kan dawakansu.

7. Ta yi karuwanci da su, dukan waɗanda suke ƙusoshin Assuriya, ta kuma ƙazantar da kanta tsakanin gumakan da ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

8. Ba ta bar karuwancinta ba, wanda ta yi tun tana a Masar, gama a lokacin 'yan matancinta mutane sun kwana da ita, sun rungumi ƙirjinta, suka biya kwaɗayinsu a kanta.

9. Domin haka na bashe ta a hannun kwartayenta, Assuriyawa, waɗanda ta yi ta kai da kawowa a cikinsu.

Karanta cikakken babi Ez 23