Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 22:12-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. A cikinka mutane suka karɓi toshi don su zub da jini. Kana ba da rance da ruwa da ƙari, kana kuma cin riba a kan maƙwabcinka saboda cutar da kake yi masa, ka kuwa manta da ni, ni Ubangiji na faɗa.

13. “‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar.

14. Zuciyarka za ta iya ɗaurewa, hannuwanka kuma za su ƙarfafa a ranar da zan gamu da kai? Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.

15. Zan watsar da kai cikin al'ummai, in warwatsa ka cikin ƙasashe, zan kawo ƙarshen mugayen ayyukanka.

16. Za a ƙasƙantar da kai a gaban sauran al'umma, sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji.”’

17. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

18. “Ɗan mutum, mutanen Isra'ila sun zama kamar ƙwan maƙera a gare ni. Dukansu sun zama kamar tagulla, da kuza, da baƙin ƙarfe, da darma, a tanderu, sun zama ƙwan maƙera na azurfa.

19. Saboda haka ni Ubangiji Allah na ce da yake dukanku kun zama ƙwan maƙera zan tattara dukanku a Urushalima.

20. Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da darma, da kuza a cikin tanderu, su hura wuta a kansu, don su narkar da su, haka zan tattara ku da zafin fushina in narkar da ku.

21. Zan tattaro ku, in hura muku wutar hasalata, za ku narke a cikinta.

Karanta cikakken babi Ez 22