Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 2:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.

8. “Amma kai, ya ɗan mutum, ka ji abin da zan faɗa maka, kada ka zama mai tayarwa kamar 'yan tawayen nan. Sai ka buɗe bakinka, ka ci abin da zan ba ka.”

9. Da na duba, sai ga hannu yana miƙo mini littafi.

10. Ya buɗe littafin a gabana, akwai rubutu ciki da baya. Ba abin da aka rubuta sai maganganun baƙin ciki, da makoki, da kaito.

Karanta cikakken babi Ez 2