Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 18:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa,‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami,Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu’?

3. “Ni Ubangiji Allah na ce, hakika, ba za a ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba.

4. Ga shi, dukan rayuka nawa ne, da ran uban da na ɗan, duka nawa ne. Wanda ya yi zunubi shi zai mutu.

5. “Ga irin mutumin da zai rayu, mutumin da yake adali, yana bin shari'a, yana kuma aikata abin da yake daidai,

6. idan ba ya cin abinci a ɗakin tsafi, bai bauta wa gumakan mutanen Isra'ila ba, bai kwana da matar maƙwabcinsa ba, ba yakan kwana da mace a lokacin hailarta ba,

7. wanda ba ya cin zalin kowa, wanda yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa, wanda ba ya ƙwace, amma yakan ba mayunwanci abinci, wanda yakan ba huntu tufa,

8. wanda ba ya ba da bashi da ruwa, ko tare da wani ƙari, wanda yake hana hannunsa yin mugunta, amma yana goyon bayan gaskiya tsakanin masu gardama,

9. wanda yake bin dokokina, yana kuma kiyaye ka'idodina da aminci, shi adali ne. Hakika zai rayu, ni Ubangiji na faɗa.

10. “Amma idan ya haifi ɗa wanda ya zama ɗan fashi, mai kisankai, yana yi wa ɗan'uwansa ɗaya daga cikin abubuwan nan, [ko shi kansa,

11. bai yi irin waɗannan abubuwa ba,] wato yana cin abinci a ɗakin tsafi, yana kwana da matar maƙwabcinsa,

12. yana kuma cin zalin matalauta masu fatara, yana yin ƙwace, ba ya mayar da abin da aka jinginar masa, yana bauta wa gumaka, yana kuma aikata abubuwa masu banƙyama,

Karanta cikakken babi Ez 18