Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 16:31-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.

32. Ke mazinaciyar mace, mai kwana da kwartaye maimakon mijinki!

33. Maza sukan ba dukan karuwai kuɗi, amma ke ce mai ba kwartayenki kuɗi, kina ba su kuɗi don su zo wurinki don kwartanci daga ko'ina.

34. Kin yi dabam da sauran mata a cikin karuwancinki, da yake ba wanda ya bi ki don yin karuwanci, ba a ba ki kuɗi, ke ce kike ba da kuɗi, domin haka kin sha bamban.”

35. Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.

36. “Ubangiji Allah ya ce, da yake kunyarki ta bayyana, an buɗe tsiraicinki cikin karuwancinki, saboda kuma gumakanki, da jinin 'ya'yanki da kika miƙa wa gumakanki,

37. domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.

38. Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina.

39. Zan bashe ki a hannun kwartayenki, za su kuwa rushe ɗakunan tsafinki, su tuɓe tufafinki, su kwashe murjaninki, su bar ki tsirara tik.

40. “Za su kuta taron mutane a kanki, za su jajjefe ki da duwatsu, su yayanka ki gunduwa gunduwa da takubansu.

Karanta cikakken babi Ez 16