Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 16:23-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. “Bayan dukan muguntarki (Kaito, kaitonki! Ni Ubangiji Allah na faɗa),

24. sai kika gina wa kanki ɗakunan tsafi a kowane fili.

25. Kika kuma gina ɗakin tsafi a kowane titi. Kin waƙala darajarki, kin ba da kanki ga kowane mai wucewa, ta haka kika yawaita karuwancinki.

26. Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi. Kin yawaita karuwancinki don ki tsokani fushina.

27. “Domin haka na miƙa hannuna gāba da ke, na rage rabonki, na ba da ke ga abokin gābanki masu haɗama, 'yan matan Filistiyawa waɗanda suka ji kunya saboda halinki na lalata.

28. “Kin kuma yi karuwanci da Assuriyawa domin ba ki ƙoshi ba. Kin yi karuwanci da su duk da haka ba ki ƙoshi ba.

29. Kin yawaita karuwancinki da Kaldiya, ƙasar ciniki, duk da haka ba ki ƙoshi ba.

30. “Kin cika uzuri,” in ji Ubangiji Allah. “Duba, kin aikata waɗannan abubuwa duka, ayyuka na karuwa marar kunya.

31. Kin gina ɗakunan tsafi a kowane titi da kowane fili. Amma ke ba kamar karuwa ba ce, da yake ba ki karɓar kuɗi.

32. Ke mazinaciyar mace, mai kwana da kwartaye maimakon mijinki!

33. Maza sukan ba dukan karuwai kuɗi, amma ke ce mai ba kwartayenki kuɗi, kina ba su kuɗi don su zo wurinki don kwartanci daga ko'ina.

34. Kin yi dabam da sauran mata a cikin karuwancinki, da yake ba wanda ya bi ki don yin karuwanci, ba a ba ki kuɗi, ke ce kike ba da kuɗi, domin haka kin sha bamban.”

35. Domin haka, ya ke karuwa, ki ji maganar Ubangiji.

36. “Ubangiji Allah ya ce, da yake kunyarki ta bayyana, an buɗe tsiraicinki cikin karuwancinki, saboda kuma gumakanki, da jinin 'ya'yanki da kika miƙa wa gumakanki,

37. domin haka zan tattara miki daga kowane waje dukan kwartayenki, waɗanda kika yi nishaɗi da su, wato dukan waɗanda kika ƙaunace su, da waɗanda kika ƙi. Zan sa su yi gāba da ke. Zan buɗe musu tsiraicinki don su gani.

38. Zan hukunta ki kamar yadda akan hukunta mata waɗanda suka ci amanar aure, suka zub da jini. Zan hallaka ki cikin zafin fushina da kishina.

Karanta cikakken babi Ez 16