Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 12:18-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Ɗan mutum, ka ci abincinka da rawar jiki, ka sha ruwanka da makyarkyata da damuwa.

19. Ka faɗa wa mutanen ƙasar, cewa ni Ubangiji Allah na ce mutanen Urushalima da suke a ƙasar Isra'ila za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suke zaune cikinta.

20. Biranen da ake zaune a cikinsu za su zama kufai, ƙasar kuma za ta zama kango, za su kuwa sani ni ne Ubangiji.”

21. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

22. “Ɗan mutum, mene ne wannan karin magana da ake faɗa a ƙasar Isra'ila cewa, ‘Kwanaki suna ta wucewa, wahayi bai gudana ba”?

23. Ka faɗa musu, ka ce ni Ubangiji Allah na ce zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra'ila ba. Amma ka faɗa musu, cewa kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.

24. “Wahayin ƙarya da dūbā na kiran kasuwa za su ƙare a Isra'ila.

25. Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

26. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

27. “Ɗan mutum, ga shi, mutanen Isra'ila suna cewa, ‘Wahayin da ya gani na wani lokaci ne can gaba, yana annabci a kan wani zamani ne na can.’

28. Domin haka ka faɗa musu, cewa ni Ubangiji na ce maganata ba za ta yi jinkiri ba, amma maganar da na faɗa za ta tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ez 12