Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 12:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.

3. Domin haka, ɗan mutum sai ka shirya kaya don zuwa zaman talala, sa'an nan ka tashi da rana a kan idonsu. Za ka ƙaura daga wurinka zuwa wani wuri a kan idonsu, watakila za su gane, cewa su 'yan tawaye ne.

4. Za ka fitar da kayanka da rana a kan idonsu, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Kai kuma da kanka za ka tafi da maraice a kan idonsu, kamar yadda mutane masu tafiyar zaman talala sukan yi.

5. Ka huda katanga a kan idonsu, sa'an nan ka fita daga ciki.

6. A gabansu za ka ɗauki kayan, ka saɓa shi a kafaɗarka, ka tafi da shi da dare. Za ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na maishe ka alama ga jama'ar Isra'ila.”

7. Na kuwa yi kamar yadda aka umarce ni. Na fitar da kayana da rana, kamar kayan mai tafiyar zaman talala. Da maraice na huda katanga da hannuwana, sa'an nan na fita da duhu, ina ɗauke da kayana a kafaɗa, a kan idonsu.

8. Da safe kuwa Ubangiji ya yi mini magana, ya ce,

9. “Ɗan mutum, ashe, mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan, ko suka ce maka, ‘Me kake yi?’

10. Ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Wannan jawabi ya shafi shugabannin Urushalima da dukan mutanen Isra'ila, waɗanda suke cikinta.’

Karanta cikakken babi Ez 12