Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Esta 4:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Mordekai ya ji dukan abin da aka yi, sai ya yage tufafinsa, sa'an nan ya sa rigar makoki, ya zuba toka a kā. Ya fita zuwa tsakiyar birni, yana ta rusa kuka da ƙarfi.

2. Ya tafi kusa da ƙofar sarki, gama ba a yarda wani ya shiga ƙofar sarki da rigar makoki ba.

3. A kowane lardi inda aka kai umarni da dokar sarki, Yahudawa suka yi babban baƙin ciki, da azumi, da kuka, da makoki. Waɗansu da yawa da rigunan makoki a cikin toka suka kwanta.

4. Sa'ad da kuyangin Esta da bābāninta suka tafi suka faɗa mata abin da Mordekai yake yi, sai sarauniya Esta ta damu ƙwarai, ta aika da riguna a sa wa Mordekai, ya tuɓe rigar makokinsa, amma Mordekai ya ƙi, bai yarda ba.

5. Sai Esta ta kirawo Hatak, ɗaya daga cikin bābānin sarki, wanda aka sa ya yi mata hidima, ta aike shi wurin Mordekai, don ya ji abin da ya faru, har ya sa yake yin haka.

6. Hatak kuwa ya tafi wurin Mordekai a dandalin birnin, a gaban ƙofar sarki.

7. Sai Mordekai ya faɗa masa dukan abin da ya faru da shi, da yawan ƙudin da Haman ya ce zai biya a sa a baitulmalin sarki don a hallaka Yahudawa.

Karanta cikakken babi Esta 4